🌐 Harshe
'Olelo Hawai'iAfaan Oromoobahasa IndonesiaBrezhonegCebuanoChamorroChichewachiShonaChongthuCiyawoDanskDeutschEestiEnglishEspañolEsperantoeʋegbeFrançaisHausaHrvatskiIgboIlocanoItalianoKikuyuKiswahiliKiyombiKreyòl AyisyenLatinaLatviešulietuviųLingálaLugandaMagyarMahasuiMāoriNederlandsNorskPohnpeianPolskiPortuguêsQach’abelRomaniRomânăSetswanaShqipsrpski jezikSuomiSvenskaTagalogTiếng ViệtTonganTwiTürkçeYorùbáÍslenskaČeštinaбеларускаяБългарскиРусскийУкраїнськаעבריתئۇيغۇرچەاردوالعربيةفارسیكوردی سۆرانیअहिराणी‎नेपालीभद्रवाही‎मराठीमानक हिन्दी‎संस्कृत भाषाहरियाणवी‎অসমীয়াবাংলাਪੰਜਾਬੀગુજરાતીଓଡ଼ିଆ‎தமிழ்తెలుగుಕನ್ನಡമലയാളംไทยဗမာἙλληνική中文日本語한국어+ Dukan Harsuna
See More Jesus
Hausa

Me Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Alheri da Mugunta? — Kashi na 2 — Gwajin Baibul

Gwajin Baibul

Me Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Alheri da Mugunta? — Kashi na 2 — Gwajin Baibul

Ga kowace ayar da take a ƙasa, zaɓi abin da ayar take koyarwa. Sakamakonka zai bayyana a ƙarshe.

Wannan ita ce jarabawar da za a yi maki. Ka ci ta domin samun ƙima zuwa Takardar Amincewar Hidimarka.

2 Korintiyawa 11:3 — Sai dai ina tsoro kada yă zama, kamar yadda maciji ya yaudari Hawwa’u da ________, ku ma a bauɗar da hankalinku daga sahihiyar biyayya amintacciya ga Kiristi.
Mai himma
nawaita
makircinsa
Farawa 3:22 — Ubangiji Allah ya kuma ce, “To, fa, mutum ya zama kamar ɗaya daga cikinmu, ya san abin da yake mai kyau da abin da yake mugu. Kada a yarda yă miƙa ________ yă ɗiba daga itacen rai yă ci, yă kuma rayu har abada.”
hannunsa
mahaifiyarsa
tafiya
Karin Magana 3:7 — Kada ka zama mai hikima a ganinka; ka ji ________ Ubangiji ka kuma guji mugunta.
girma
horo
tsoron
Ibraniyawa 5:13 — Duk wanda yake rayuwa a kan madara, shi kamar ________ ne har yanzu, kuma bai san ainihi mene ne ya dace ba.
labulen
jariri
horon
1 Tessalonikawa 5:22 — ku ƙi kowace ________.
mugunta
wahala
ƙarfin
Ayyukan Manzanni 10:38 — yadda Allah ya shafe Yesu ________ da Ruhu Mai Tsarki da kuma iko, da kuma yadda ya zaga ko’ina yana aikata alheri yana kuma warkar da dukan waɗanda suke ƙarƙashin ikon Iblis, domin Allah yana tare da shi.
Tarshish
Yahudiya
Banazare
3 Yohanna 1:11 — Abokina ƙaunatacce, kada ka yi ________ da abin da yake mugu sai dai abin da yake nagari. Duk mai yin abin da yake nagari daga Allah yake. Duk mai yin abin da yake mugu bai taɓa sanin Allah ba.
almajiransa
ikkilisiyoyi
koyi
Zabura 34:14 — Juyo daga ________ ku yi alheri; nemi salama ku kuma yi ƙoƙarin samunta.
tawaye
mugunta
bautar
Zabura 37:27 — Ku juyo daga ________ ku yi alheri; sa’an nan za ku zauna a ƙasar har abada.
tawaye
mugunta
bautar
Ru'uya ta Yohanna 2:7 — Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ________. Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi ikon ci daga itacen rai, da yake cikin aljannar Allah.
hatimi
tauraron
ikkilisiyoyi
Farawa 1:31 — Allah ya ga dukan abin da ya yi, yana da kyau ƙwarai. Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta ________ ke nan.
shida
sau
biyar
Romawa 10:17 — Saboda haka, bangaskiya takan zo ne ta wurin jin ________, akan ji saƙon kuma ta wurin maganar Kiristi.
saƙo
taƙama
rami
Farawa 3:6 — Sa’ad da macen ta ga ’ya’yan itacen suna da kyau don abinci, abin sha’awa ga ido, abin marmari kuma don samun hikima, sai ta tsinka ta ci, ta kuma ba da waɗansu wa ________ wanda yake tare da ita, shi ma ya ci.
murya
iyalin
mijinta
Mai Hadishi 4:12 — Ana iya ________ ƙarfin mutum ɗaya, mutum biyu za su iya kāre kansu. Igiya riɓi uku tana da wuya tsinkawa.
al’ul
daɗi
shan
Ishaya 7:14 — Saboda haka Ubangiji kansa zai ba ku alama. Ga shi ________ za tă yi ciki, za tă haifi ɗa, za tă kuwa kira shi Immanuwel.
budurwa
ɗamara
reshen
1 Yohanna 3:8 — Duk mai aikata abin da yake zunubi shi na Iblis ne, domin Iblis mai aikata zunubi ne tun ________. Dalilin da ya sa Ɗan Allah ya bayyana kuwa shi ne don yă rushe aikin Iblis.
safe
farko
maɓulɓular

← Koma zuwa nazarin