Me Ya Kamata Ni Yi Domin Ceto? — Rayuwa da Ita — Gwajin Baibul
Ga kowace ayar da take a ƙasa, zaɓi abin da ayar take koyarwa. Sakamakonka zai bayyana a ƙarshe.
Wannan ita ce jarabawar da za a yi maki. Ka ci ta domin samun ƙima zuwa Takardar Amincewar Hidimarka.
Romawa 6:17 — Amma godiya ga Allah don ko da yake a dā ku bayi ne ga ikon zunubi, da dukan zuciyarku kun yi biyayya ga irin ________ da aka danƙa muku.
maƙwabcinsa
yar’uwar
koyarwar
Yoshuwa 1:8 — Kada ka bar Littafin ________ nan yă rabu da bakinka, sai dai ka yi ta tunani game da shi dare da rana, don ka lura, ka yi duk abin da aka rubuta a ciki, ta haka ne za ka yi nasara cikin duk abin da za ka yi.
annoba
Dokokin
rauni
1 Yohanna 1:7 — Amma in muna tafiya cikin haske, yadda yake cikin haske, muna da zumunci da juna ke nan, kuma ________ Yesu, Ɗansa, yana tsarkake mu daga dukan zunubi.
jinin
Tentin
lokacin
Ibraniyawa 10:24 — Bari kuma mu yi tunani a kan yadda za mu gargaɗe juna ga ________ da kuma ayyuka nagari.
bayyana
ƙauna
tuna
Romawa 13:11 — Ku yi wannan domin kun san irin zamanin da kuke ciki. Lokaci ya yi da za ku ________ daga barcinku, don cetonmu ya yi kusa yanzu fiye da lokacin da muka fara ba da gaskiya.
asirin
haƙuri
farka
Luka 14:28 — “In wani daga cikinku yana so ya gina gidan sama, ai, yakan fara zama ne, ya yi lissafin abin da ginin zai ci tukuna, don yă ga ko yana da isashen ________ da zai gama ginin.
kuɗi
jaririn
ruwan
Ayyukan Manzanni 2:42 — Suka ba da kansu ga koyarwar ________ da kuma ga zumunci, ga gutsuttsura burodin da kuma ga addu’a.
manzanni
dattawan
annabawa
Luka 8:15 — Amma irin da suka fāɗi a ƙasa mai kyau kuwa, su ne mutane masu kyakkyawar ________, mai kyau, da suka ji, suka riƙe, suka kuma jimre har suka ba da ’ya’ya.”
bakin
haikali
zuciya
Romawa 6:11 — Haka ku ma, ku ɗauke kanku ________ ne ga ikon zunubi amma rayayyu cikin tarayya da Allah cikin Kiristi Yesu.
matattu
kabari
mace
Mattiyu 1:21 — Za tă ________ ɗa, za ka kuma sa masa suna Yesu, gama shi ne zai ceci mutanensa daga zunubansu.”
haifi
ribar
nemi
Filibbiyawa 2:12 — Saboda haka, ya ________ ƙaunatattu, kamar yadda kullum kuke biyayya ba kawai sa’ad da ina nan ba, amma yanzu da ba na nan tare da ku, ku ci gaba da yin ayyukan cetonku da tsoro da kuma rawan jiki,
bayyana
abokaina
rayuwar
← Koma zuwa nazarin