🌐 Language
'Olelo Hawai'iAfaan Oromoobahasa IndonesiaBelarusianBrezhonegCebuanoChamorroChichewachiShonaChongthuCiyawoDanskDeutschEestiEnglishEspañolEsperantoeʋegbeFrançaisHausaHrvatskiIgboIlocanoItalianoKikuyuKiswahiliKiyombiKreyòl AyisyenLatinaLatviešulietuviųLingálaLugandaMagyarMahasuiMāoriNederlandsNorskPohnpeianPolskiPortuguêsQach’abelRomaniRomânăSanskritSetswanaShqipsrpski jezikSuomiSvenskaTagalogTiếng ViệtTonganTwiTürkçeUyghur tiliYorùbáÍslenskaČeštinaБългарскиРусскийУкраїнськаעבריתاردوالعربيةفارسیكوردی سۆرانیअहिराणी‎नेपालीभद्रवाही‎मराठीमानक हिन्दी‎हरियाणवी‎অসমীয়াবাংলাਪੰਜਾਬੀગુજરાતીଓଡ଼ିଆ‎தமிழ்తెలుగుಕನ್ನಡമലയാളംไทยဗမာἙλληνική中文日本語한국어+ Dukan Harsuna
See More Jesus
Hausa

Menene Littafi Mai Tsarki Yake Cewa Game da Sani? — Rayuwa Da Shi — Gwajin Baibul

Gwajin Baibul

Menene Littafi Mai Tsarki Yake Cewa Game da Sani? — Rayuwa Da Shi — Gwajin Baibul

Ga kowace ayar da take a ƙasa, zaɓi abin da ayar take koyarwa. Sakamakonka zai bayyana a ƙarshe.

Wannan ita ce jarabawar da za a yi maki. Ka ci ta domin samun ƙima zuwa Takardar Amincewar Hidimarka.

Karin Magana 1:7 — Tsoron Ubangiji shi ne masomin ilimi, amma wawaye sun rena hikima da ________.
horo
masifa
biya
Karin Magana 2:4 — in ka neme shi yadda ake neman ________ ka kuma neme shi kamar yadda ake neman ɓoyayyiyar dukiya
abinci
baƙin
azurfa
Karin Magana 2:5 — to, za ka gane ________ Ubangiji ka kuma sami sanin Allah.
tsoron
horo
farin
Yaƙub 1:5 — In waninku ya ________ hikima, ya kamata yă roƙi Allah, mai bayarwa hannu sake ga kowa ba tare da gori ba, za a kuwa ba shi.
laifi
rasa
hukunta
Karin Magana 18:15 — Zuciya mai la’akari kan nemi sani; kunnuwan mai ________ kan bincika don yă koya.
magana
mugunta
hikima
Zabura 94:10 — Shi da yake yi wa ________ horo ba ya hukunci ne? Shi da yake koya wa mutum ba shi da sani ne?
al’ummai
rana
farin
Zabura 25:9 — Yakan bi da masu ________ cikin abin da yake daidai ya kuma koyar da su hanyoyinsa.
tawali’u
cikakke
wauta
Hosiya 6:3 — Bari mu yarda da Ubangiji; bari mu nace gaba don mu yarda da shi. Muddin rana tana fitowa, zai bayyana; zai zo mana kamar ruwan bazara, kamar ruwan saman ________ da yake jiƙe ƙasa.”
farko
fara
girmama
Yohanna 7:17 — Duk wanda ya zaɓi yin nufin Allah, zai ________ ko koyarwata daga Allah ce, ko kuwa don kaina ne nake magana.
bayyana
gane
cika
Mattiyu 11:29 — Ku ɗauki karkiyata a kanku, ku kuma yi koyi da ni, gama ni mai ________ ne marar girman kai, za ku kuwa sami hutu don rayukanku.
cikakke
hukuncin
tawali’u
2 Bitrus 3:18 — Sai dai ku yi girma cikin ________ da sanin Ubangijinmu da Mai Cetonmu Yesu Kiristi. A gare shi ɗaukaka ta tabbata yanzu da har abada! Amin.
alheri
farko
dole
2 Bitrus 1:5 — Saboda haka, ku yi iyakar ƙoƙari ku ƙara wa ________ nagarta; ga nagarta kuwa, ku ƙara mata sani;
bangaskiyarku
haifa
annabi
Karin Magana 10:14 — Mai hikima kan yi ajiyar sani, amma ________ wawa kan gayyaci lalaci.
ƙarfi
bakin
kunya
Karin Magana 15:14 — Zuciya mai la’akari kan nemi sani, amma bakin wawa ________ ce ke ciyar da shi.
wauta
haƙuri
shan
Kolossiyawa 1:10 — Ta haka za ku yi rayuwa wadda ta dace da Ubangiji, ku kuma ________ shi a ta kowace hanya, kuna yin aiki mai kyau ta kowace hanya, kuna kuma yin girma cikin sanin Allah.
bautar
gamshe
haƙuri
Filibbiyawa 1:9 — Addu’ata ita ce ƙaunarku tă yi ta cin gaba da ƙaruwa cikin ________ da kuma zurfin ganewa
kaɗai
sani
farko
1 Korintiyawa 8:1 — To, game da abincin da aka miƙa hadaya ga ________ kuwa. Mun san cewa dukanmu muna da ilimi. Ilimi yakan kawo girman kai, amma ƙauna takan gina.
tsarkaka
harsuna
gumaka
Karin Magana 3:6 — cikin dukan hanyoyinka ka ________ da shi, zai kuwa sa hanyoyinka su miƙe.
rawanin
ado
amince
Zabura 119:66 — Ka koya mini sani da kuma hukunci mai kyau, gama na gaskata a ________.
hanyoyinsa
umarnanka
zukatansu
Karin Magana 24:5 — Mutum mai hikima yana da iko sosai, kuma mutum mai ________ yakan ƙaru da ƙarfi;
adalci
sani
ƙauna
2 Korintiyawa 10:4 — Makaman da muke yaƙi da su, ba ________ na duniya ba ne. Sai dai na ikon Allah ne, masu rushe wuraren mafaka masu ƙarfi.
iyayensu
labarin
makamai
2 Korintiyawa 10:5 — Muna ka da masu gardama da kowane ________ ɗaga kai da yake kafa kansa gāba da sanin Allah, muna kuma jan hankalin kowa ga bautar Kiristi.
wuraren
tunanin
cinikinki
2 Korintiyawa 4:6 — Domin shi Allah wanda ya ce, “Bari haske yă haskaka daga ________,” ya sa haskensa ya haskaka a cikin zukatanmu, don yă ba mu hasken sanin ɗaukakar Allah a fuskar Kiristi.
ƙauna
tuna
duhu
Afisawa 6:17 — Ku kuma ɗauki ________ kwano na ceto, da takobin Ruhu, wato, Maganar Allah.
hular
ƙeta
haƙuri
Malaki 2:7 — “Gama ya kamata leɓunan firist su kiyaye ilimi, ya kamata kuma mutane su nemi umarni daga bakinsa, domin shi ne manzon Ubangiji ________.
al’ummai
Maɗaukaki
kwana
Karin Magana 15:2 — ________ mai hikima kan yi zance mai kyau a kan sani, amma bakin wawa kan fitar da wauta.
tsawata
Harshen
amfani
1 Bitrus 3:15 — Sai dai a cikin zukatanku ku keɓe Kiristi a matsayin Ubangiji. A kullum, ku kasance a shirye ku ba da amsa ga duk wanda yake neman ku ba da dalilin wannan begen da kuke da shi. Amma ku yi wannan cikin ________ da ladabi
sauƙinkai
cikakke
tawali’u
2 Timoti 2:15 — Ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka gabatar da kanka a gaban Allah a matsayin wanda aka amince da shi, ma’aikaci wanda ba shi da dalilin jin kunya wanda kuma yake ________ kalmar gaskiya daidai.
rayuwar
fassara
tuba
Daniyel 11:32 — Ta wurin ________ baki zai gurɓata waɗannan da suka karya alkawari, amma mutanen da suka san Allahnsu za su yi tsayin daka su yi jayayya da shi.
amfani
daɗin
shuka

← Koma zuwa nazarin